Kamar kowane kasuwanci, nasara a kiwon awaki tana buƙatar shiri, ilimi, da kuma tsari mai kyau.
Kafin ki sayi akuya na farko, wajibi ne ki fahimci waɗannan abubuwa guda 13. Wannan shine cikakken jagoran da zai kiyaye ku daga asara kuma ya kai ku ga nasara a harkar kiwon awaki.
NA FARKO: Kafin Ki Kawo Awaki Gida (Shirye-Shiryen Farkon Farawa)
1. IRI DA ZAƁI (BREEDS AND SELECTION)
Wannan shine mataki na farko kuma mai mahimmanci. Me kike son samu daga kiwon awakin?
Idan Kina Neman Nama: Zaɓi irin awaki masu saurin girma kuma masu yawan nama kamar su Boer Goat ko wasu irin awaki na gida masu ƙarfi kamar west African dwarf ko Red Sokoto, Kano brown ko sahel.
Idan Kina Neman Madara: Zaɓi irin awaki kamar su Saanen ko Nubian, waɗanda aka san su da samar da madara mai yawa da kuma inganci.
Ki tabbatar kin zaɓi awaki masu lafiya, masu ƙarfin jiki, kuma waɗanda ba su da alamun cuta a lokacin siye. Ki kula da idanunsu da kuma yanayin gashin jikinsu. Zaifi kyau ki je siya tare da wanda yake da ilimi akan awaki sosai.
2. GINI DA SHINGE (HOUSING AND FENCING)
Awaki suna buƙatar wurin kwana mai tsabta, busasshe, kuma mai kariya.
Ga abubuwan da ya kamata a kula:
• Kariya daga Yanayi: Dole ne matsugunin ya kare su daga ruwan sama, zafin rana, da iska. Wuri mai ɗan tudu zai fi dacewa don gudun taruwar ruwa.
• Tsabta: Tabbatar cewa ana tsaftace wurin a kai a kai. Wurin da yake da laka ko danshi yana haifar da cututtuka.
• Shinge Mai Ƙarfi: Awaki suna da wayo kuma suna son tsalle. Wajibi ne a samar da shinge mai ƙarfi da tsawo don hana su fita, da kuma kare su daga barayi.
3. TSARIN KASUWANCI (BUSINESS PLANNING)
Kada ki fara kiwo a matsayin kawai wani abu. Ki fara shi a matsayin kasuwanci.
• Kuɗin Farawa (Startup Costs): Da farko Ki lissafa kuɗin sayan awaki, gina matsuguni, sayen abinci, da kuma allurar rigakafi.
• Riba da Asara: Yi hasashen kuɗin shiga daga sayar da nama ko madara da kuma kuɗin fita na shekara.
• Dabarun Haɓaka kiwon: Menene burinki bayan shekara ɗaya ko biyu? Neman ƙara yawan awakin ne ko kuma canzawa zuwa samar da wani abu na daban kamar sarrafa madarar awakin?
4. DOKOKIN GWAMNATI (LEGAL REQUIREMENTS)
Kafin ki fara kiwon, ki tabbatar kin san dokokin yankinku.
• Izini (Permits): Wasu yankuna suna buƙatar izini don kiwon dabbobi masu yawa.
• Kiyaye Mahalli: Ki tabbatar cewa kiwon naki bai haifar da wani abu da zai cutar da maƙwabta ba, kamar wari ko amo mai yawa.
NA BIYU: Kula da Awaki Cikin Inganci (Management)
5. ABINCI MAI GINA JIKI (NUTRITION)
Abinci shine tushen lafiya da kuma ingancin samar da nama ko madara
• Ciyawa da Ganye (Forage): Wannan shine babban abincin awaki. A tabbatar sun samu isasshen ciyawa mai kyau.
• Hatsi (Grains): Hatsi kamar masara, dawa, ko garin gyada ana buƙata, musamman ga awaki masu shayarwa ko kuma waɗanda ake son su yi kiba da sauri.
• Supplements: Dole ne a ba su ma'adanai da sauran sinadarai na vitamins, da gishiri wanda suke ƙara musu ƙarfi, da Kuma wainda zasu taimaka wajen ƙarfin ƙasusuwa da kuma lafiyar jikin su baki daya.
• Ajiye Abinci (Feed Storage): A tabbatar ang ajiye abincin a busasshen wuri, a cikin buhu da za'a rufe bakin, domin kare shi daga danshi, bera, da kuma ƙwari.
6. SAMAR DA RUWA (WATER SUPPLY)
Awaki suna buƙatar ruwa mai tsafta koyaushe. Rashin ruwa yana kawo lahani ga lafiyarsu da kuma rage samar da madara.
• Tsafta: Ki riƙa wanke kwano ko robar ruwansu a kowace rana don kiyaye tsaftar ruwan.
• Samarwa: Ki tabbatar sun samu ruwa mai yawa, musamman a lokacin zafi ko kuma lokacin da suke shayarwa.
7. KULA DA LAFIYA (HEALTH MANAGEMENT)
Fahimtar alamun cuta yana iya ceton ki daga babban asara.
• Allurar Rigakafi: Yi aiki tare da likitan dabbobi don samar musu da allurar rigakafi da maganin tsutsar ciki a lokutan da suka dace.
• Alamun Cututtukan Yau da Kullun: Nemi alamun gudawa, rashin cin abinci, zazzabi, ko kuma tari.
• Killace sabon dabba (Quarantine): Idan kin sayo sabon akuya, ki ajiye shi a wani wuri na daban na tsawon kwanaki 14-30 kafin ki haɗa shi da tsofaffin awakin.
• Killace dabba Mai ciwon(Isolation): ki Killace dabbar da aka ga ta fara nuna alamun wasu cututuka a ɗaki daban.
8. KULA DA KIWO (PASTURE MANAGEMENT)
Idan kina da ƙasa mai faɗi don kiwo, dole ne ki kula da ita.
• Raba Kiwo: Raba filin kiwon zuwa sassa daban-daban don awakin su riƙa kiwo a sashi ɗaya bayan wani. Wannan zai bai wa sauran sassan damar sake fitar da sabuwar ciyawa.
• Ciyayi Masu Guba: a cire dukkan ciyayi masu guba waɗanda ke da haɗari idan awaki suka ci su.
9. KWAREWAR KIWO (HERDING SKILLS)
Koyan yadda za a gudanar da kiwon awaki yana nufin sanin halayensu.
• Awaki suna son bin juna. Kada a yi ƙoƙarin tsoratar da su, maimakon haka, a jagorance su cikin natsuwa.
• Kulawa ta Musamman: Ki koyi yadda za a kula da ƙafafunsu (hoof trimming) da kuma yadda za a gyara ko rage musu ƙaho (dehorning) idan ya zama dole.
NA UKU: Ci Gaba da ƙaruwar Riba (Growth and Profit)
10. HAYAYYAFA DA HAIHUWA (BREEDING AND REPRODUCTION)
Hayayyafa shine tushen bunƙasar gona.
• Lokutan da akuya zata iya daukan ciki: Ki fahimci lokacin da akuyoyinki ke shiga yanayin daukan ciki (wato lokacin da suke neman bunsuru).
• Lokacin da Ya Fi Inganci na Haɗa Akuya da bunsuru: Mafi kyawun lokacin da za a haɗa akuya (doe) da bunsuru (buck) shine lokacin da take cikin sha'awa (estrus cycle). Kuma lokacin nan yana kasance wa ne a duk bayan 18-21 days. Wannan lokaci ya fi zama mai amfani tsakanin awa 12 zuwa 36 bayan bayyanar alamun sha’awar ta farko.
Don gane alamun sha'awa ki kula da waɗannan alamomi:
i. Rashin Natsuwa da yawan yawo.
ii. Ƙara, Yawan Kira ko iwo (bleating).
iii. Vulva zai kumbura ko ya kasance yana da danshi.
iv. Yawan Watsa Wutsiya (tail wagging) ko jijjigata ta.
Yadda Ake Haɗawa Mai Inganci:
Haɗa akuya da bunsuru sau biyu a cikin wannan lokacin na sha'awa na iya ƙara yawan damar ɗaukar ciki.
Idan kin gano alamun sha'awar a Yamma, ki haɗa ta da bunsuru gobe da Safe.
Idan kin gano alamun sha'awar da Safe, ka haɗa ta da bunsuru da Yamma na wannan ranar.
• Tsarin Ciki: Lokacin ɗaukar ciki zuwa haihuwa na akuya yana kusan kwanaki 150 (kimanin watanni 5).
• Kula da Ƙananan Awaki: Bayan haihuwa, yaran awaki suna buƙatar kulawa ta musamman, suna Buƙatar su sami madarar farko (colostrum) da kuma kariya daga zafi da sanyi.
11. AJIYE BAYANAN KASUWANCI (RECORD-KEEPING)
Babu wani kasuwanci da zai ci gaba ba tare da ajiye bayanai ba.
• Bayanan Kuɗi: Ajiye bayanan dukkan kuɗin shiga da kuma kuɗin fita.
• Bayanan Lafiya: Rubuta ranar da aka yi wa kowace akuya allura ko magani.
• Bayanan Samarwa: Ga awakin madara, ki rubuta yawan madarar da kowace akuya ke samarwa. Wannan zai taimaka wajan gane waɗanda suke samarwa sosai da kuma waɗanda ba su yi.
12. SANIN KASUWA (MARKET)
Kafin ki siyar da awakin ki ko Madara, ki san inda za ki sayar da kuma farashin da ya dace.
• Buƙatun mutane: Shin akwai buƙatu mafi yawa na naman awaki a yankinki, ko kuma madara ce?
• Farashi: Bincika farashin kasuwa na yau da kullun don kada ki sayar da arha.
Kiwon awaki na iya zama mai daɗi da kuma riba idan har ki ɗauki kowanne mataki da hankali. Ki fara da ƴan awaki kaɗan, a hankali Zaki ringa fahimtar su da Kuma karin ilimi mai yawa akan kiwon, sannan ahankali ki faɗaɗa gonarki.
Shin kuna da wata tambaya game da kiwon awaki? Rubuta mana a sashin comment! 👇





0 Comments