Kabeji yana da matuƙar mahimmanci a kasuwa, kuma yana ɗaya daga cikin kayan lambu da ke samar da riba mai kyau ga manoma. Amma kamar yadda ake cewa, kabeji yana son yanayi mai sanyi da kuma kulawa ta musamman.
Idan kina so ki ga manya-manyan kabeji masu ƙarfi, dole ne a bi matakan noma da suka dace. Bari muyi duba akan matakai 6 da za'a bi don samun nasara. tun daga shirya ƙasa har zuwa lokacin girbi.
1. SHIRIN WURI DA ƘASA (SOIL PREPARATION)
Kafin ki fara shuka, aikin farko shine a shirya wurin shukan kabejin yadda ya kamata.
• Zaɓin Wuri: Zaɓi wuri a gonarki da yake samun rana akalla awanni 6 a kullum. Wannan yana da mahimmanci don ƙarfafa ganye da kuma samar da kai mai nauyi.
• Ingancin Ƙasa: Kabeji yana bunƙasa ne a cikin ƙasa mai laushi, wadda ruwa ke ratsawa cikin sauƙi (well-drained), kuma take da wadataccen takin gargajiya (organic matter). Idan ƙasarki tana riƙe da ruwa, sai ki samar mata da wata hanyar da ruwan zai riƙa wucewa.
• Amfani da Taki: Saka takin gargajiya (kamar taki ko kashin kaji) mai yawa a cikin ƙasar kafin fara shuka. Wannan zai tabbatar da cewa ƙasan ta yi ƙarfin da zai ɗauki kabeji har zuwa girbi.
2. SHUKA IRI (STARTING SEEDS)
• Lokacin Shuka: Kabeji yana son sanyi, don haka yana da kyau a fara shuka iri a cikin seed tray ko kuma a gida (nursery). A fara wannan aikin makonni 4 zuwa 6 kafin lokacin da za a dasa shi a gona (wato kafin lokacin damina ta fara tsayawa ko kuma lokacin da yanayi ya yi sanyi sosai). Kamar daga October zuwa April.
• Zurfin Shuka: Idan za a shuka kai tsaye, a binne iri a cikin rami mai zurfin 1cm zuwa 2cm kawai, sannan a rufe da ƙasa a hankali.
• Tabbatar da Danshi: Tabbatar cewa ƙasar shukar tana da ɗan danshi a koyaushe don ba da damar shukar ta fito da ƙarfi.
3. JUYAWA ZUWA BABBAN GONA (TRANSPLANTING)
Wannan mataki ne mai hatsari, amma yana da mahimmanci.
• Alamun da za'a lura: Idan shukar kabejin ta kai girman ganye 4 zuwa 5, kuma ta tsayi har inci 4 zuwa 6, ta yi shiri don transplanting.
• Tazarar Shuka (Spacing): Wannan shine sirrin samun manya-manyan kawunan kabeji. Dole ne a samar da isasshen fili ga kowace shuka:
A shuka kowace shuka da tazarar inci 12 zuwa 24 a tsakaninta.
Layukan kuma ya kamata su kasance da tazarar inci 24 zuwa 36.
• Zuba Ruwa bayan transplanting: Ki ba ta ruwa da yawa nan ta ke bayan an yi shukar don taimaka wa shukan don ta zauna da kyau a sabon wurinta.
4. KULA DA SHUKA (MAINTENANCE)
Kabeji tana san taki mai yawa kuma tana buƙatar ruwa mai yawa.
• Ruwa Akai-akai: Kabeji tana buƙatar ruwa akai-akai. Kada a bari ƙasan ta bushe. Musamman a lokacin da shukar take farawa da samar da kai. Idan ta rasa ruwa a wannan lokacin, kawunansu za su yi ƙanana kuma za su fashe.
• Taki Mai Ƙarfi: Kabeji tana buƙatar taki mai wadataccen Nitrogen. Bayan juyawa zuwa gona, a sake ba ta wani taki mai ƙarfin Nitrogen (kamar Urea ko NPK) bayan kamar makonni 3 zuwa 4. Wannan zai ƙarfafa ganyen kuma ya sa kawunan su yi saurin girma.
• Cire Ciyawa: Ciyawa ce abokin gaba na farko. Tana cin duk wani abinci da kabeji take buƙata (taaki da ruwa) a tabbatar an riƙa cire ciyawa a ko'ina akai-akai.
5. YAƘI DA ƘWARI DA CUTUTTUKA (PEST CONTROL)
Kabeji tana da daɗi ga mutane, amma kuma tana da daɗi ga ƙwari!
• Sanin Maƙiya: Ƙwari kamar su Cabbage Worms (waɗanda suke tauna ganye) da kuma Aphids (waɗanda suke shan ruwan ganye) na iya haifar da babbar asara.
• Kariya: Ka riƙa duba ganyen kabejinka a kullum don gano alamun ƙwari.
• Magani: Za a iya amfani da maganin kashe ƙwari na gargajiya (idan kina noman gargajiya) ko kuma maganin ƙwari mai inganci wanda aka yarda da shi, idan abin ya yi yawa.
6. LOKACIN GIRBI (HARVESTING)
• Alamun Girbi: Ana girbe kabeji ne idan kawunansu sun yi katun-katun, sun yi tauri, kuma suna da nauyi idan kin danna su da hannunki. Idan kabejin ya fara fashewa ko ya taushi, ya wuce lokacin girbi.
• Yadda Ake Yanke: Yi amfani da wuka mai kaifi sosai. Yanke kan a jikin tushen kabejin, ki bar kusan inci biyu na ganye a jikin kabejin. Wannan yana taimakawa wajen tsawaita rayuwar kabejin bayan girbi.
• Ci Gaban Girbi: Idan an yanke babban kan kabejin, kada a cire tushen. Wasu lokuta, idan an bar tushen, zai sake fitar da kananan kawunan kabeji waɗanda za a iya girbe su daga baya.
Wannan shine jagorar da za ta taimaka muku samun nasara wajen noman kabeji a gida ko a gona. Da fatan za'a gwada noman kabeji.
Shin kina da wata tambaya game da taki ko yadda za a yaki ƙwari a gonarki? Rubuta mana a sashin comment! 👇


0 Comments